
Ƙasar Benin ta samu damar hawa kan jadawalin rukunin da ya kunshi Najeriya da Rwanda da Zimbabwe da Afrika ta Kudu da kuma Lesotho a gasar sharar fagen neman kaiwa ga shiga gasar cin kofin duniya na ƙwallon ƙafa.
Benin wacce tayi wasan ta a ranar Alhamis da kasar Zimbabwe ta hada maki 8 daga wasanni 5, biyo bayan tashi daga wasa tsakanin ta da Zimbabwe kowacce ƙasa na da ci biyu.
A gobe juma’a ne dai za’a fafata tsakanin Rwanda, wacce ke a matsayi na biyu a rukunin da maki 7 da kuma Najeriya wacce ke s matsayi na biyar da maki 3 a Kigali babban birnin Rwanda yayin da Afrika ta Kudu wacce ke da maki 7 za ta kara da ƙasar Lesotho.









