
Hukumar ƙwallon ƙafa ta CAF, ta dakatar da mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ƙasar Tanzania, Adel Amrouche, tsawon wasanni takwas biyo bayan zargin da yayi na cewa Morocco na da tasirin gaske akan CAF kuma ƙasar na taka rawa wajen zaɓen alkalan wasanni.
Tanzania dai ta sha kashi a hannun ƙasar Morocco a wasan zagayen na biyu na gasar cin kofin Nahiyar Afrika da ƙasar ta ke karbar bakuncin sa.
Amrouche wanda ya bayyana takaice kan yadda ƙasar Morocco ke taka rawa akan al’amuran da suka shafi hukumar CAF.
Tuni dai hukumar ta CAF ta musanta zargin, tana mai cewa alhakin ta ne zaɓen alkalan wasa da zasu yi alkalanci a yayin wasa, kuma tana da tsari da ka’ida ta take amfani wanda babu son rai a cikin sa.
Sai dai kuma jin kadan bayan wadannan kalamai, hukumar CAF ta bada sanarwar dakatar dashi na tsawon wasannin takwas, kafin daga bisani, hukumar ƙwallon ƙafa ta Tanzania ta bada sanarwar sallamar sa daga aiki.









