LabaraiWasanni

An bayyana sunan Alkalin wasan da zai jagoranci wasan Najeriya da Algeriya

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika CAF, ta ayyana sunan alkalin wasan da zai jagoranci wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa Super Eagles za tayi da Deserts Foxes na Algeriya.

A cewar rohotannni, Omar Artan, Alkalin wasa daga ƙasar Somalia,shine zai jagoranci alkalanci wasan Najeriya da Algeriya.

Rohotannni sun bayyana Omar Artan, a matsayin fitattacen alkalin wasa, kuma ya jagoranci da dama daga cikin wasannin a ciki da wajen nahiyar Afrika.

Najeriya dai za ta fafata wasan matakin dab dana kusa dana ƙarshe watau Quarter Finals da ƙasar Algeriya a ranar Asabar mai zuwa da misalin karfe biyar na yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button