LabaraiWasanni

CAF za ta ɗage gasar AFCON na 2027

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) na duba yiwuwar ɗage Gasar Kofin Nahiyar Afirka da aka shirya gabatarwa a shekarar 2027.

A cewar bayanai da ke fitowa daga hedkwatar hukumar da ke birnin Alkahira, ƙasar Masar, yunkuri ɗage gasar na da nasaba da sabon tsarin jadawalin wasanni da CAF ta aiwatar kwanan nan, wanda ake sa ran zai daidaita gasar a kan tsarin zagayowar shekaru huɗu, inda aka tsara fara aiwatar da sabon tsarin a shekarar 2028.

Sakamakon wannan sauyin jadawali, CAF na nazarin shirin matsar da gasar daga shekara ta 2027 zuwa shekarar 2028.

Tun da farko dai, an ba ƙasashen Tanzania da Uganda da kuma Kenya damar yin haɗin gwiwar karɓar baƙuncin gasar.

Ana sa ran CAF za ta fitar da matsaya ta ƙarshe a cikin watanni masu zuwa, bayan kammala shawarwari da ƙasashen da ake sa ran zasu karbi bakuncin gasar da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button