LabaraiSiyasa

Tsohon gwamnan jihar Waziri Tambuwal ya amsa gayyatar EFCC

A cewar jaridar Telegraph, hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal zuwa ofishin ta domin neman karin bayani akan waɗansu kuɗaɗen da yawan su ya kai Naira biliyan dari da tamanin da tara da ake zargin an fidda da su daga asusun banki, lamarin da ya sabawa dokar mu’amala da kuɗaɗe na shekarar 2022.

A cewar jaridar, Tambuwal ya isa ofishin hukumar ta EFCC da ke Abuja da misalin karfe sha daya da rabi na safe, a inda ya fuskanci tambayoyi daga masu bincike akan zargin da ake masa.

Sai dai kuma da jaridar ta neman jin ta bakin mai magana da yawun hukumar EFCC, , Dele Oyewale, ya ƙi amincewa ya ce komai akan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button