
Rohotanni sun bayyana cewa, dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya samu mafaka tare da iyalinsa a gidan gwamnatin jihar Bayelsa.
A cewar rohotanni tun bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya ayyana dokar-ta-baci a jihar Rivers sakamakon rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar, ake tunanin akan inda dakataccen gwamnan ya nufa.
Sai dai kuma yanzu rya tabbata cewa gwamnan jihar Bayelsa Duoye Diri, shine ya bawa Siminalayi Fubara da iyalan sa mafaka a gidan gwamnatin jihar Bayelsa.









