LabaraiSiyasa

Kotun Koli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin Sakataren jam’iyyar PDP na Kasa.

Kotun Koli Najeriya ta tabbatar da Samuel Anyanwu, a matsayin halastaccen Sakataren Jam’iyyar PDP na Kasa.

Tun farko dai, Samuel Anyanwu, wanda na hannun daman Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesome Wike ne, ya ɗaukaka kara akan hukuncin da Kotun ɗaukaka kara ta yanke akan matsayin sa na Sakataren jam’iyyar PDP biyo bayan tsaya wa takarar neman kujerar gwamnan jihar Imo.

A hukuncin da Kotun koli ta yanke a wannan rana ta Juma’a ta amince da hujjojin da ɓangaren Samuel Anyanwu, suka gabatar ba cewa kotun ɗaukaka kara da kuma babban kotun jihar Enugu basu da hurumin sauraren shari’ar domin lamari ne na cikin gida da ya shafi jam’iyyar PDP kawai, a don haka kotun koli tayi watsi da hukunci da kotun ɗaukaka kara ta yanke wanda ya bayyana Udey-Okoye, a matsayin sakataren jam’iyyar tare da tabbatar da Samuel Anyanwu akan matsayi sa na Sakataren jam’iyyar PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button