LabaraiLafiya

WHO ta musanta ikirarin alakanta cutar galahanga da maganin Paracetamol

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta musanta ikirarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa shan maganin zazzaɓi na Paracetamol a lokacin da mace ke da juna biyu na haifar da cutar matsalar ƙwaƙwalwa wato galahanga.

WHO ta ce babu wata hujja a kimiyyance da ta tabbatar da iƙirarin shugaban na Amurka.

Cikin wata sanarwa da hukumar Lafiyar ta duniya ta wallafa a shafinta na intenet, ta ce akwai tarin biciken kimiyya masu yawa da aka gudanar cikin shekaru 10 da suka gabata, amma babu wanda ya taɓa tabbatar da alaƙar cutar galahanga da kuma maganin na Paracetamol.

WHO ta shawarci mata masu juna biyu su ci gaba da bin shawarar likitocinsu, waɗanda su ke taimaka musu ta hanyar ba su maganin da ya kamata su sha.

A cewar hukumar lafiyar kowane magani na da ƙa’idar da ake bi wajen shansa, musamman a watanni ukun farkon kowane juna-biyu, kuma ana sha ne bisa shawarar likitoci.

A makon da ya kamata ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wani jawabi game da cutar, galahanga, inda ya ce ta fara yawaita a Amurka, yana mai cewa dole gwamnatinsa ta ɗauki mataki bayan gano musabbabinsa.”

Wasu bincike da aka gudanar sun alaƙanta shan sinadarin acetaminophen – wanda shi ne asalin sinadarin da ke cikin Paracetamol – da cutar kwakwalwa, amma binciken ba su fayyace alaƙar ba, da kuma irin illar da maganin ke yi.

A cewar hukumar lafiyar matsalar galahanga na daga cikin manyan matsalolin lafiya da ta ke bai wa fifiko a ayyukanta kuma ake yawan tattauna ta a manyan tarukanta na duniya.

Alƙaluman hukumar sun nuna cewa kusan mutum miliyan 62 ne a duniya ke fama da matsalar galahanga – da ake samu sakamakon wasu matsaloli masu alaƙa da ƙwaƙwalwa.

Duk da ƙaruwar kiraye-kirayen wayar da kai da ake yi game da matsalar a shekarun baya-bayan nan, WHO ta ce har yanzu ba a gano haƙiƙanin abin da ke haifar da matsalar ba, kodayake an fahimci abubuwa da dama ne ke haifar da matsalar.

Daga ƙarshe hukumar Lafiyar ta duniya ta ce tana jajanta wa masu fama da lalurar a faɗin duniya tare da kira ga mutane su guji ƙyamar masu lalurar, saboda kowa da irin ƙaddarar lalurar da ubangiji ke jarrabarsa da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button