
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta cika sharruddan sayen dan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bournemouth, Dan ƙasar Ghana, Antoine Semenyo.
Rohotannni sun bayyana cewa Antoine Semenyo, zai koma Manchester City bayan ƙungiyar Bournemouth ta amince da tayin £65m da Manchester City ta gabatar.
Tuni dai rohotannni suka bayyana cewa za’a gudanar da duba lafiyar ɗan wasa a gobe Alhamis bayan kammala wasan da ƙungiyar Bournemouth za tayi da Tottenham a ranar Laraba.









