
Dan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, wanda ke taka leda a matsayin aro a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray, Victor Osimhen, ya sha alwashin cigaba da zama a ƙungiyar duk da raɗe-raɗin da ake yi na cewa wasu fitattun ƙungiyoyi daga kasar Ingila da suka hada da Manchester United da Arsenal da kuma Chelsea na zawarcin sa.
Victor Osimhen wanda ya kara tabbatarwa da Galatasaray tabbacin cigaba da taka musu leda bayan dawowar sa ƙungiyar daga hutun Kirsimeti, ya kuma bayyana aniyyar sa na ganin cewar ya taimakawa kungiyar ta samu nasarar da ake bukata a wannan kakar wasannin.
Zuwa yanzu dai Victor Osimhen ya zurawa Galatasaray Ƙwallaye goma sha biyu tare da taimakawa wajen zura Ƙwallaye biyar a wasanni goma sha biyar da ya fafatawa ƙungiyar.
Victor Osimhen na zaman aro ne a ƙungiyar ta Galatasaray daga Napoli.









