LabaraiWasanni

Wasannin mako na 24 na gasar Premier League

A yau Gasar Premier League na ƙasar ke shiga makon na 24, kuma a wasannin da za’a gabatar a ranar Asabar, Nottingham Forest da a makon da ya gabata tayi rashin nasara a hannun Bournemouth da ci biyar da nema, za ta karbi bakuncin Brighton, yayin da ƙungiyar da ke jan ragamar gasar Liverpool za ta fafata da Bournemouth.

Newcastle wacce ke kan matsayi na 5 a gasar za ta fafata da Fulham, yayin da Southampton wanda dukkanin alamu ya nuna za ta iya samun kanta a gasar championship a badi za ta ziyarci Ipswich.

Filin wasa na Goodison Park, zai karbi bakuncin wasa tsakanin Everton da Leicester City, a wani wasa da ya ke da matukar muhimmanci ga dukkanin ƙungiyoyin biyu ne neman cigaba da kasance a gasar ta firmimiya.

Aston Villa wacce ke fama da rashin lafiyar zaratan yan wasan ta biyar za ta ziyarci za ta kasance a filin wasa na Molineux, domin fafatawa da Wolves.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button