Labarai

Hukumar Kidaya:Mun yi wa yara miliyan 10 rijista cikin watanni uku a Najeriya

Hukumar ƙidaya ta Najeriya (NPC) ta ce ta yi wa yara miliyan goma rijista tare da ba su takardar shaidar haihuwa a cikin watanni ukun da suka gabata.

Shugaban hukumar, Alhaji Nasir Isa Kwara ne ya faɗi hakan ga manema labarai bayan uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta miƙa takardar shaidar haihuwa ga jaririyar da aka fara haifa a shekarar 2025 a babban asibitin Asokoro da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Shugaban hukumar na ƙasa wanda ya samu wakilcin Kwamishan tarayya ta hukumar daga jihar Katsina, Bala Banya, ya bayyana cewa baza suyi ƙasa a gwiwa ba waje tabbatar da cewa duk jaririn da aka haifa a Najeriya anyi masa rijista kuma an bashi takardar shaidar haihuwa.

” Mun ɗau wani lokaci muna wannan aikin, kuma a watanni ukun baya, munyi wa yara da basu kai shekara 1 ba zuwa ƴan shekara 5 su miliyan 10 rijista. A yanzu kuma za mu mayar da hankali kan yara ƴan ƙasa da shekara ɗaya” a cewar shi.

Ya kuma ce sabbin shaidar haihuwar wanda akeyi ta yanar gizo na zuwa ne da lambar shaidar zama ɗan ƙasa wato NIN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button