
A yau za’a gabatar da wasan kusa dana ƙarshe na gasar cin kofin zakarun ƙungiyoyin ƙwallon kafa na kasar Spain da ake gabatar a birnin Jeddah dake ƙasar Saudiyya.
Wasan wanda za’a gabatar dashi tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid da Mallorca, zaayi shine a filin wasa na Sarki Abdullahi dake Jeddah.
Tarihin fafatawa tsakanin ƙungiyoyin biyu na nuni da cewa sun fafata wasanni 31 a tsakanin ƙungiyoyin biyu, kuma Real Madrid ita ce tafi rinjaye a yawan samun nasara, a inda ta samu nasara a wasanni 22, yayin da Mallorca ta samu nasara a wasanni 6 aka kuma yi canjaras a wasanni 3.









