
Ana sa ran a cikin wata mai zuwa na Fabrairu, hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya za ta yanke hukunci akan korafin da Najeriya ta shigar gaban ta, tana zargin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da amfani da’yan wasan da basu da cikakkiyar shaidar zama yan ƙasar a wasan sharar fagen neman kaiwa ga shiga gasar cin kofin duniya da ƙasashen biyu suka fafata a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.
Najeriya tayi rashin nasarar ne a wasan ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan kammala wa’adin lokacin wasa dukkanin ƙasashen biyu na da ci daya.
Sai dai kuma bayan kammala wasa, hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF tayi zargin cewar akwai yan’wasan da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo tayi amfani dasu waɗanda basu cika ka’idar zama yan ƙasa ba bisa la’akari da dokokin ƙasar.








