Farashin kaya na cigaba da sauka a Najeriya.

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta c e hauhawar farashin kaya ya sauka a cikin watan Faburairun bana.
Sanarwar da hukumar ta fitar a yau Litinin ta ce alƙalumman da ta tattara game da hauhawar farashin kayayyaki a cikin watan da ya gabata sun nuna cewa an samu rage akan kuɗin kayan da kusan kaso ashirin da uku cikin dari.
Hukumar ta NBS ta kuma bayyana cewa an samu raguwar tashin farashin kayayyaki idan aka kwatanta da yadda lamarin ya ke a farkon wannan shekarar ta 2025.
A shekarar da ta gabata dai, an yi fama da tashin farashi kayayyaki a tarihin Najeriya, wanda ake ganin an shafe shekara 28 ba a taɓa fuskantar irin shi ba, bayan shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin mai da kuma karya darajar naira.
A watan jiya ma babban bankin Najeriya, CBN ya ƙayyade kuɗin ruwa a kashi 27.5 bisa ɗari, inda ta kafa hujja da tashin farashi.









