Labarai

Wani Alkali ya hallaka kansa a harabar kotu a ranarsa ta karshe na aiki.

Wani alkali mai suna Stephen Yekel a jihar Georgia da ke kasar Amurka ya hallaka kansa ta hanyar harbin kansa da bindiga a harabar kotunsa.

Yekel wanda ya ke da shekaru 74 a duniya, an hango gawarsa ne a harabar kotun Effingham a safiyar ranar Talata, ranar da take kasancewa ranarsa ta karshe na aiki.

A cewar jaridar Daily Mail, rohotanni sun yi nuni da cewa Stephen Yekel yayi amfani da bindiga ne ta hanyar harbin kansa, sai dai hukumomi na cigaba da bincike domin tabbatar da hakan.

Stephen Yekel a yayin rayuwarsa ta aiki, ya kasance mai aiki tukuru, kuma ya kwashe sama da shekara 46 yana aikin Shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button