Kotun ta ci tarar budurwar saboda rashin amsa gayyatar saurayin ta a jihar Osun.

Wata kotun majistare da ke zamanta a Ilesa, a jihar Osun ta ci tarar wata budurwa Naira dubu dari da hamsin N150,000 biyo bayan samun ta da laifin kin amsa gayyatar saurayin ta, bayan ta karbi Naira dubu uku N3,000 daga wajen sa a matsayin kuɗin mota.
Budurwar mai suna, Rhoda Adu, ta karbi N3,000 daga wajen Mr Olapitan a matsayin kuɗin abin hawan da za ta hau domin amsa gayyatar da yayi ma ta zuwa wajen sa.
Sai dai kuma bayan karbar kuɗin ne, sai budurwa Rhoda ta kashe wayar ta, kuma dukkanin kokarin Olapitan na samun ta a waya yaci tura.
Ganin cewar an yaudare shi ya sanya Olapitan garzaya wa ofishin Yansanda na Ayeso, inda ya shigar da jirage yana neman abu masa hakkin sa.
Daga nan ne Yansanda suka cika aikin su, inda kuma bayan bincike suka gurfanar da budurwa Rhoda a gaban kotu tare da shaidar N3,000 da Olapitan ya aike wa Rhoda a matsayin shaida.
Bayan sauran bangarorin biyu, Alkali kotun majistaren, Akogun Oludare, ya yanke hukunci cewar Rhoda ta mayarwa da Olapitan kuɗin sa N3,000, kuma ta biya shi naira dubu dari N100,000 a matsayin diyyar saba yarjejeniyar da tayi, sa’annan kuma ta biya shi naira dubu hamsin a matsayin diyya na hali rashin jin dadi da ta sa shi a sakamakon karya yarjejeniyar da tayi.









