
A yau za’a fara gabatar da gasar cin kofin zakarun ƙungiyoyin ƙwallon kafa na kasar Spain.
Gasar dai wacce ta ƙunshi ƙungiyoyin hudu da suka hada da Athletic Club da Barcelona da Real Madrid da kuma Mallorca, za’a gabatar da ita ne a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.
A wasan farko da za’a fafata yau, Athletic Club za ta fuskanci Barcelona a filin wasa na Sarki Abdullah dake Jeddah.
Karawar ta yau za ta kasance karo na 62 da ƙungiyoyin biyu ke fafatawa da juna, kuma daga cikin wannan adadin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ita ce ke da rinjaye samun yawan nasara, a inda tayi nasara a wasanni 39, Athletic Club ta samu nasara a wasanni 9, aka kuma yi canjaras a wasanni 13.
Sai dai kuma wani abin ban mamaki shine yadda Barcelona ta sanya sunayen yan wasan ta biyu Dani Olmo da Pau Victor cikin ayarin yan’wasa duk da cewa a yanzu basu da rijista da hukumomi ƙwallon ƙafa a Spain.









