LabaraiWasanni

FIFA ta fidda jadawalin matsayin ƙasashen duniya a ƙwallon ƙafa

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta fidda sabon jadawalin matsayin ƙasashe a ƙwallon ƙafa.

Kamar yadda jadawalin ya nuna, Najeriya ta samu cigaba daga matsayi na talatin da takwas 38 zuwa na ashirin da shida 26.

Jadawalin wanda FIFA ta fitar a ranar Litinin, ya kuma dora Najeriya a matsayin ƙasa ta uku 3, a ƙwallon ƙafa a nahiyar Afrika.

Har zuwa yanzu dai ƙasar Morocco ita ce ke jan ragamar ƙasashen Afrika a ƙwallon ƙafa, yayin da take kan matsayi na takwas (8) a duniya.

Senegal ita ce ta kasance ƙasa ta biyu a nahiyar Afrika, kuma ta ke kan matsayin ƙasa ta goma sha biyu a duniya.

Ƙasar Algeriya ita ce ta kasance a matsayin ƙasa ta hudu a nahiyar Afrika, yayin da Masar ke biye mata baya a matsayin ƙasa ta biyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button