LabaraiLafiya

ABIN TAUSAYI: Wata mata ta yanke jiki ta fadi, kuma nan take rai yayi halinsa a tashar mota Abuja.

Wata mata ta yanke jiki ta fadi a tashar mota da ke babban birnin tarayya Abuja a daidai wurin da ake hawa motocin da ke tafiya jihar Benue.

Matar mai suna Alice Emmanuel ta gamu da ajalin na ta ne a ranar Laraba 1 ga watan Janairu yayinda da take kokarin sauko wa daga motar hayar da ta kawo ta tashar mota da misalin karfe 9 minti 25 na safiya.

Ganin faruwar lamarin ya sa manajan tashar sanar da yan’sanda halin da ake ciki, a inda bayan garzayawa da ita asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa rai yayin halin sa.

Da ya ke karin haske, mai magana da yawun rundunar yansanda reshen babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya tabbatar da faruwar lamarin, a inda ya kara da cewa tuni rundunar ta tuntubi iyalan matar domin sanar dasu abin da faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button