
Hukumar dake kula da yanayi ta Kasa NiMet, tayi harsashin cewa akwai yiyuwar samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na tsawon kwanaki uku, a wasu daga cikin jihohi kasar nan.
A cewar NiMet, akwai yiyuwar jihohi kamar Cross River da Aka Ibom da Edo da Bayelsa da Delta da kuma Ogun su fuskanci samu ruwan sama daga ranar Laraba 9 ga watan Afrilu zuwa ranar Juma’a 11 ga wata.
Hakazalika, hukumar ta NiMet, tayi harsashin samun matsakaicin ruwan sama a jihohin Legas da Ondo da Delta da Imo da Abia da kuma Ekiti.
Hukumar tayi kuma gargadi cewar akwai yiyuwar samun iska mai karfi gaske, a don haka ta shawarci matafiya dasu kasance cikin shirin tare da kiyaye sharudan tuƙi a yayin ruwan sama.









