LabaraiWasanni

Barcelona ce a kan gaba a iya ƙwallo a gasar Laliga – a cewar Kocin Atletico Simeone.

Kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atletico Madrid, Diego Simeone, ya bayyana ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona a matsayin ƙungiyar da tayi zarra wajen wasan a tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Laliga

Diego Simeone wanda ya bayyana haka ne bayan kammala wasan hamayya na Madrid Derby da ƙungiyar sa ta Atletico Madrid tayi da Real Madrid, a inda aka kamalla wasa kowacce ƙungiya na da ci daya.

A cewar Simeone, salon wasan da Barcelona ke amfani dashi a bana ya sha bambam da na sauran ƙungiyoyi ta yadda suke iya amfani da duk wata dama da suka samu wajen kai farmaki a cikin kyakkyawan yanayin wasan ƙwallon ƙafa.

Kunnen doki da Real Madrid tayi da Atletico Madrid zai faranta wa magoya bayan Barcelona, duba da cewa hakan zai basu damar rage tazarar da ke tsakanin ta da ƙungiyoyin biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button