Ba daidai ba ne, EFCC ta dinga karɓe wayoyin hannun mutane kafin basu damar shiga ofishin su – inji Kotu.

Babbar kotu a jihar Oyo, ta yanke hukunci cewar ya sabawa doka matakin da hukumar hana yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa ta EFCC ke yi na karɓe wayoyin hannun mutane kafin basu damar shiga ofishin su.
Da yake yanke hukunci akan karar da wani lauya mai suna Adedeji Falujo, ya shigar a gaban kotu, mai Shari’a, Oluwaseun Toluwanimi Ademola Salami, yayi bayanin cewar matakin hukumar ta EFCC na karbe wayoyin hannun masu ziyara ofis din su ya ci karo da tanadin yancin ɗan Adam na walwala da sadarwa kamar yadda ya ke a ƙunshi a cikin sashi na 39 na ƙundin tsarin mulki Najeriya na shekarar 1999.
Da yake gabatar da korafin sa, Adedeji Falujo, ya bayyanawa kotun cewa hukumar ta EFCC ta tilasta masa ajiye wayoyin sa na hannun gabanin bashi damar shiga ofishin ta, lamarin da sanya masu neman sa da dama suka gaza samun sa a waya.









