LabaraiWasanni

Everton ta kammala ɗaukar David Moyes a karo na biyu

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta kammala ɗaukar David Moyes a matsayin kocin ƙungiyar a karo na biyu.

Mai shekara 61, ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyu da rabi a Goodison Park, bayan da ƙungiyar ta kori Sean Dyche a ranar Alhamis.

Yanzu haka Everton na matsayi na 16 a kan teburin Premier, bayan da ta yi nasara sau uku kacal a wasa 19 da ta buga a kakar bana.

Za’a ƙulla yarjejeniyar tsare iyakokinsu tsakanin Lebanon da Syria.

Bayan sanya hannu a ƙungiyar, sabon kocin ɗan asalin Scotland ya alƙawarta mayar da Everton kan ganiyarta musamman a gasar Premier.

David Moyes ya taɓa horas da Everton daga 2002 zuwa 2013 kafin ya koma Manchester United.

Sai dai ya raba gari da United bayan wata 10 kacal, inda ya koma Real Sociedad daga bisani ya koma Sunderland sai kuma West Ham.

Kocin ya kasance ba shi da ƙungiya tun bayan barin West Ham, wadda ya ɗaukar wa kofin Europa Conference League a 2023

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button