LabaraiWasanni

Guardiola ya bayyana ƙungiyoyi huɗu da suke da damar ɗaukar kofin zakarun nahiyar turai.

Bayan doke ƙungiyar sa daga gasar zakarun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na nahiyar turai, Champions League, Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana Real Madrid a matsayin daya daga cikin ƙungiyoyi da suke da damar ɗaukar kofin gasar a wannan shekarar.

A cewar Pep Guardiola, kamar kowacce shekara, Real Madrid na a sahun gaba wajen samun damar lashe wannan gasar.

Pep Guardiola ya kuma bayyana Barcelona da Paris Saint Germain PSG da kuma Liverpool cikin jerin ƙungiyoyin da suke da damar lashe gasar a wannan shekarar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button