LabaraiWasanni

Wasan karshen na gasar Italy Super Cup tsakanin AC Milan da Inter Milan, waye zai yi nasara?

A yau za’a gabatar da wasan karshe na gasar zakarun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa kasar Italy da ake wa lakabi da Italian Super Cup da kasar Saudiyya ta karbi bakuncin sa.

Wasan karshen wanda za’ayi tsakanin Inter Milan da AC Milan za’a gabatar da shine a filin wasa na Al-Awwal na jami’ar Sarki Saud dake a Riyadh wanda ke iya ɗaukar yan’kallo dubu ashirin da biyar.

Wasan dai zai kasance na hamayya tsakanin ne ƙungiyoyin biyu, kuma karawar ta wannan rana za ta kasance karo na 68 da suke fafatawa a tarihi, a inda Inter Milan ke kan gaba da rinjaye yawan samun nasara a wasanni 32, Ita kuwa AC Milan tayi nasara a wasanni 22, aka kuma yi canjaras a wasanni 13.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button