LabaraiSiyasa

SIYASA; Shugabannin Jam’iyyar APC sun kaiwa Buhari ziyara.

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce duk wata haɗaka da jam’iyyun hamayyar ƙasar ke shirin yi da nufin kawar da APC a zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba.

Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai a jihar Kaduna lokacin ziyarar – da ya jagoranci shugabannin jam’iyyar wajen kai wa tsohon shugaban ƙasar – Muhammadu Buhari.

Gabanin ziyarar su Gandujen, tawagar jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar tare da tsoffin gwamnonin jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da Sanata Ahmed Makarfi da kuma Sanata Aminu Waziri Tambuwal ta fara kai wa Buhari ziyara a gidan nasa.

Ganduje ya ce ziyarar su Atikun ba ta ɗaga musu hankali ba, saboda a cewarsa ”suna son ƙulla wata haɗaka da ba za ta yi tasiri ba”.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya ce a shirye suke kuma sun san yadda za su ɓullo wa lamarin kodayake ya ce ba zai faɗi dabarar da za su bi ba.

Ganduje ya ce duk da cewa a yanzu haka APC na da iko da jihohin ƙasar 21, har yanzu jam’iyyarsu na hangen ƙarin wasu jihohin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button