LabaraiWasanni

Simone Inzaghi yayi sallama da Inter Milan.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Milan, ta bada sanarwar da ke cewar mai horar da ƙungiyar, Simone Inzaghi, ya ajiye aikin sa.

Ajiye aikin na Simone Inzaghi, na zuwa ne, kwanakin kaɗan bayan rashin nasarar da yayi a wasan ƙarshe na cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai a hannun Paris Saint Germain PSG, da ci biyar da nema.

Inzaghi, mai shekaru 49 a duniya, ya jagoranci Inter Milan lashe gasar Siriya ‘A’ sau daya, tare da kai ƙungiyar ga wasan ƙarshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, Champions League har sau biyu, haka kuma ƙungiyar ta Inter Milan ta lashe gasar kalubale ta Coppa Italiya har sau biyu tun bayan shekara ta 2021, da ya karbi aikin horar da ƙungiyar.

A wata sanarwa daga shugaban ƙungiyar, Guiseppe Marotta, ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya da Inzaghi tare da amincewa da buƙatar sa na barin aiki ba tare da ba ta lokaci.

Rohotannni dai na nuni da cewa, Inzaghi zai nufi ƙasar Saudiyya ne domin karba aikin horar da ƙungiyar Al Hilal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button