
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan,ta bada sanarwar sallamar mai horarwar da yan wasan ta, Sergio Conceicao.
A wata sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana matakin sallamar Sergio Conceicao, daga aiki, a matsayi wani canji da aka samu a tsarin tafiyar da ƙungiyar zuwa mataki na gaba.
AC Milan ta kuma yabawa, Sergio Conceicao, bisa gudunmawar da ya bayar wajen ciyar da ƙungiyar gaba, tare da yi masa fatan alheri.
AC Milan dai ta naɗa Sergio Conceicao a matsayin kociyan ta ne a watan Disamba shekarar da ta gabata, akan yarjejeniyar shekaru biyu.
Sai dai kuma koma bayan da kungiyar ta samu, na rashin samun gurbin shiga gasar zakarun nahiyar turai a karshe gasar Siriya’A’ da aka kamalla, ya sanya ƙungiyar ɗaukar matakin sallamar Sergio Conceicao daga aiki, a inda ake harsashin cewar ƙungiyar za ta maye gurbin sa da tsohon kociyan ta Massimiliano Allegri.









