LabaraiSiyasa

Jama’ar Bauchi ne za su zaɓar mini magaji’ – inji Gwamnan Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Bala Mohammed ya ce ba zai yi gaban kansa ba wajen zaɓar wanda zai gaje shi a zaɓen 2027.

Mafi yawa dai ya zamo kamar wata al’ada ga gwamnonin jihohi da ke wa’adin mulki na biyu, su shige gaba wajen ganin naɗin ƴan takara da kuma shigewa gaba domin ganin dole sai shi ne zai gaje su bayan sun kammala mulkinsu.

Gwamnonin sukan kafa hujjar yin hakan ne da buƙatar ganin an ci gaba da aiwatar da ayyukan da suka faro ko kuma kwaɗayin ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya a karkashin tutar jam’iyyarsu.

To sai dai a hirar sa da BBC, gwamna Bala Mohammed ya ce baya da ra’ayin irin waccan al’ada ta gwamnonin Najeria.

Gwamnan ya ce jama’ar jihar Bauchi ne, musamman masu ruwa da tsaki a siyasance za su tantance wanda ya dace ya gaje shi a ƙarshen wa’adin mulkin nasa, kamar yadda shi ma aka yi masa a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button