LabaraiWasanni

Manchester United ta kai ga zagaye na gaba na gasar kalubale na FA Cup.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta Kai ga zagaye na hudu na gasar cin kofin kalubale na ƙasar Ingila FA Cup biyo bayan nasarar da ta samu akan Arsenal a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan kammala wasa kowacce ƙungiya na da ci daya a tsakanin su.

Ɗan wasan tsakiyar fili na Manchester United Bruno Fernandes shine ya fara zura ƙwallo a raga a minti na 52 yayin da ɗan wasan baya Gabriel ya ramawa Arsenal ƙwallon ta a minti na 63. Haka kuma sakamakon ya kasance har zuwa karin lokaci na mintuna 30.

Daga nan ne aka kuma bugu daga kai sai mai tsaron raga a inda Manchester tayi nasara zura ƙwallayen ta biyar, Arsenal kuma ta zubda guda ta hannun Kai Havertz.

A sauran wasanni da aka gabatar na gasar, Crystal Palace ta lallasa Stockport County da ci daya da nema, Ipswich ta doke Bristol Rovers da ci uku da nema, Newcastle tayi nasara akan Bromley da ci uku da daya, yayin da Swansea ta sha kashi a hannun Southampton da ci uku da nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button