LabaraiLafiya

Za’a samu karin masu ɗauke da cutar kansa a duniya zuwa sama da miliyan 30 nan da shekara ta 2030.

Wani sabon rahoto kan cutar kansa ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2050 mutum miliyan 30 da rabi za su kamu cutar a duniya.

Rahoton na mujallar lafiya ta ‘The Lancet’ ya ce ƙasashe matalauta ne matsalar za ta fi shafa inda aka yi hasashen samun ƙaruwar cutar da samun yawan mace-mace.

Rahoton ya ce za a samu ƙaruwar masu cutar kansa da kashi 61 zuwa 2050.

Hasashen binciken ya ce mutum sama da miliyan 30 za su kamu da ciwon na kansa a 2025 daga mliyan 19 da aka yi hasashe a shekarar 2024.

Binciken ya ce hakan zai faru ne saboda ƙaruwar yawan jama’a a duniya.

Binciken ya kuma yi hasashen cewa sama da mutum miliyan 18 ne ciwon na kansa zai kashe inda adadin zai kai kusan kashi 75 cikin dari .

Rahoton ya yi nazari ne kan nau’ikan ciwon kusan 47 a ƙasahse 204 tare da bibiyar yawaitar mace-mace daga 1990 zuwa 2023 wanda ya bayar da damar yin hasashen zuwa shekarar 2050.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button