LabaraiLafiya

An kaddamar da kwamitin kwararru da zai sa ido akan samar da ingantaccen jini ga marasa lafiya a jihar Kano

A kokarin ta na kawo karshen matsalolin da ake fuskanta wajen tabbatar da kyakkyawan yanayin samar da jini ga marasa lafiya da kuma kulawa da ajiyar sa, gwamnatin jihar Kano ta samar da wani kwamitin kwararru da zai sa ido akan yadda ake gudanar da ayyukan bada jini da kuma ajiyar sa domin marasa lafiya.

Da yake kaddamar da kwamitin, Kwamishina lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa gwamnati tayi tunani samar da kwamitin kwararrun ne domin tabbatar da inganci da kuma tsarin da ake bi wajen samar da jini ga marasa lafiya da je bukatar ƙarin jini a jikin su.

Dakta Abubakar Labaran ya kuma bayyana kyakkyawan zaton da yake dashi na ganin cewar za’a samu nasarar da ake bukata duba da ƙunshin membobin kwamitin wanda ya ce a zaɓo sune bisa cancanta da kwarewar sa a fannin kiwon lafiya

Kwamishina na lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano karkashin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa kulawa da muhimmancin da take bawa fannin lafiya a ko da yaushe.

Da yake jawabi a madadin mambobin kwamitin, daraktan kula da al’amurran lafiya na asibitocin jihar Kano, Dr Musbahu Rabiu ya godewa Kwamishina na lafiya bisa kyakkyawan zaton da yake yi musu, tare da tabbatar masa cewa kwamitin zai yi aiki tukuru don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button