LabaraiWasanni

Barau FC za ta fafata da Wikki Tourists don neman tikitin shiga gasar Firimiya Lig ta ƙasa.

WASANNI

A gobe ne idan Allah ya kaimu za’a gabatar da zagaye na biyu na wasannin sharar fagen neman kaiwa ga shiga gasar Firimiya Lig ta kasa da ake gabatarwar a tsakanin ƙungiyoyin takwas da aka raba zuwa rukuni biyu watau arewa da kuma Kudancin Najeriya.

A wasanni zagaye farko, daga shiyyar arewa, Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga Kano tayi canjaras da Yobe Desert Stars, yayin da aka kuma tashi daga wasa babu ƙungiyar da tayi nasarar zura ƙwallo a raga tsakanin Wikki Tourists daga Bauchi da Doma United daga Gombe.

A shiyyar kudu, Osun United ta doke Warri Wolves da ci daya da nema, yayin da Crown FC ta sha kashi a hannun Kun Khalifa da ci daya da nema.

A zagaye na biyu na wasannin da za’a gabatar a gobe Litinin, a rukunin ƙungiyoyin da suka fito daga arewacin Najeriya da misalin tara na safe, Doma United za ta kara da Yobe Desert Stars yayin da za’a fafata tsakanin Barau FC da Wikki Tourist da misalin karfe sha daya na safe.

A rukunin kungiyoyin da suka fito daga kudu, Kun Khalifa za ta kara da Warri Wolves da misalin karfe biyu na rana, yayin da Crown FC za ta hadu da Osun United da karfe hudu na yamma

Ana dai gabatar da wasannin ne a filin wasa na Stephen Kesho dake birnin Asaba a jihar Delta, kuma Ƙungiyoyi biyun farko ne dai daga kowanne rukuni zasu haura zuwa gasar firimiya lig ta kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button