LabaraiWasanni

Ku biya ni albashi na, kafin ku sallame ni – inji Kocin Super Eagles, Eric Chelle.

Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, Eric Chelle, ya bayyana cewa ya kamata hukumar ƙwallon ƙafa ta Kasa NFF ta biya shi albashin sa, kafin ta sallame shi.

A watan Janairun da ta gabata ne dai Eric Chelle, wanda da asalin ƙasar Mali ne, ya karbi aikin horar da Super Eagles, sai dai kuma duk da kyakkyawan fatan da NFF ke dashi a kansa, ƙungiyar na cikin tsaka-mai-wuya a ƙoƙarin ta na neman kai wa ga gasar cin kofin duniya da za’a gabatar a ƙasar Amurka, musamman ma biyo bayan rashin tabuka abin arziki da yayi a gasar da ya jagorancin yan wasan gida na Super Eagles zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afrika. Lamarin da ya sa aka fara jita-jitar sallamar sa daga aiki.

Zuwa yanzu dai Najeriya na a matsayi na hudu a rukunin ‘c’ ne neman kai ga shiga gasar cin kofin duniya, kuma a wata mai zuwa ƙungiyar za ta karbi bakuncin Ruwanda kafin daga bisani ta ziyarci kasar Afrika ta Kudu domin karawa da Bafana Bafana a ranar 9 ga watan Satumba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button