
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, dan ƙasar Argentina, Lionel Messi, ya bayyana shakku kan ko zai iya wakiltar ƙasar sa, a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za’a gabatar a shekara mai zuwa a ƙasar Amurka.
Messi wanda ya bayyana hakan a ƙarshen wasan da Argentina ta lallasa Venezuela da ci uku da nema, ya kara da cewa zai yi nazarin akan yanayin jiki da kuma kuzarin sa kafin yanke hukuncin ƙarshe akan halartar gasar.
Wasan Venezuela ya kasance wasa sharar fagen neman shiga gasar cin kofin duniya na ƙarshe da Messi ya wakilci Argentina a ƙasar sa ta haihu, kuma shine yayi nasara zura ƙwallaye biyu daga cikin ukun da Argentina ta samu.
Zuwan yanzu dai, tauraron wasan ƙwallon ƙafan na duniya, ya wakilci ƙasar Argentina a wasanni 193, ya kuma zura wa ƙasar ƙwallaye 114.









