
Jami’an tsaro sun Kama wani mutum da ke zaune a yankin Abagana sake karamar hukumar Njikoka dake jihar Anambra, wanda ake zargi da kwararawa matar fetur tare da cinna ma ta wuta biyo bayan zargin cewar tana cin amanar sa.
Lamarin dai a cewar jaridar Vanguard ya faru ne a ranar Talata a wani kauye mai suna Eziezekwe dake karamar hukumar ta Njikoka.
Matar sai suna Chioma Nwana ta gamu da ajalinta ne sakamakon raununkan da ta samu bayan an garzaya da ita asibiti.
Shaidun gani da ido sun shaidawa jaridar Vanguard cewa, hatsaniya tsakanin ma’auratan ta samu samu asali ne sakamakon zargin da mijin yayi wa matar sa na cewa ta na zuwa wajen wani saurayin ta.
Bayan faruwar lamarin mijin matar ya mika kansa ga ofishin Yansanda na Abagana, tare da sanar musu da ta’asar da ta aikata yana mai cewa yayi haka ne domin wuce haushin sa akan yadda matar ta sa ta je yawon zubar masa da mutunci.









