LabaraiWasanni

Me ya kamata Ku sani kan fafatawa tsakanin Liverpool da Tottenham.

A daren yau za’a gabatar da zagayen farko na wasan kusa dana ƙarshe watau semi finals na gasar Carabao Cup tsakanin, Tottenham da kuma Liverpool a filin wasa na Tottenham Hotspur Stadium.

Wasan na yau, zai kasance karo na 64 da ƙungiyoyin biyu ke fafata wasa a tsakanin su, kuma daga wannan adadi, Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ita ce da rinjaye samun mafi yawan nasara, a inda tayi nasara a wasanni 34, Tottenham ta samu nasara a wasanni 14, aka kuma yi canjaras a wasanni 16, aka kuma zura ƙwallaye 190.

Za’a gabatar da zagaye na biyu na wasan a ranar Alhamis 6 ga watan Fabrairu a filin wasa na Anfield.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button