Labarai

Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci rufe shafukan batsa na intanet

Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci hukumar sadarwa ta ƙasar NCC da ta umurci kamfanonin da ke samar da intanet su rufe duk wasu shafukan intanet da ke nuna hotuna ko bidiyon batsa cikin gaggawa.

Majalisar ta cimma matsayar ne bayan wani ƙudiri da ɗanmajalisa daga jihar Katsina, Dalhatu Tafoki, ya gabatar.

Tafoki ya bayyana cewa bidiyoyin batsa da ke intanet na zama babbar matsala a duniya, kuma zuwa yanzu Najeriya ba ta ɗauki wani matakin magance matsalar ba.

Ya ce Najeriya ƙasa ce mai “addini”, inda manyan addinan ƙasar suka haramta batsa da kuma nuna tsiraici.

Ɗanmajalisar ya kuma bayyana gargaɗin da masana halayyar ɗan’adam suka yi kan mummunan tasirin da kallon bidiyon batsa ke da shi, ciki har da yiwuwar karfafa yin zina, da karuwanci, da kuma kasa rabuwa da kallon ta.

Majalisar ta kuma buƙaci hukumar NCC ta hukunta duk kamfanin samar da intanet da ya ƙi bin umarnin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button