LabaraiLafiya

Mutane miliyan 3,700,000 na fuskantar barazanar yunwa a yankin arewa maso gabas.

Ƙungiyar agaji ta ICRC ta bayyana cewar akwai yiwuwar fuskantar matsalar yunwa a arewa maso gabashin Najeriya sakamakon tashin hankalin da ya tilastawa manoma kauracewa gonakin su.

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar mai ɗauke da sanya hannun kakakin ta Aliyu Dawobe ta ce akalla mutane miliyan 3,700,000 ke fuskantar barazanar ƙarancin abinci a yankin, kuma cikin su harda wasu manoman da a baya ke ci da al’umma.

ICRC ta ce tashe tashen hankulan da aka kwashe shekaru ana yi a yankin, ya tilasta wa mutane da dama tserewa daga gidajen su da kuma hana su zuwa gonakin su domin samar da abinci.

Yayin da damin ta fara zama da gindinta a yankin, kayan abinci kuma suka fara ƙarewa, yanzu haka iyalai na fuskantar barazana, abinda ke tilasta musu zuwa kasuwa domin sayen abinci.

Shugabar hukumar ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, ta ce wannan yanayi kan tilastawa iyalai rage abincin da suke ci, saboda karancinsa ko kuma rashin kudi.

A cewar ta domin tinkarar wannan matsala, ICRC ta shirya wani tallafin noman da zai shafi noman rani da na damina, waɗanda akalla gidaje dubu 21,000 suka amfana ta hanyar samun tallafin iri mai inganci da kuma kayan aiki.

Tallafin ya kuma kunshi kayan abinci irin su shinkafa da tumatir da kuɓewa, baya ga horar da manoman a kan dabarun noma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button