
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta fidda sunayen yan wasan da zasu fafata da Osasuna a wasan farko na gasar Laliga ta wannan shekarar da za’a gabatar a ranar Talata.
Jerin sunayen yan wasan ya ƙunshi masu tsaron raga uku da suka hada da Courtois da Lunin da kuma matashin mai tsaron raga mai shekaru 20 Sergio Mestre.
Yan wasan baya sun hada da Carvajal da Militao da Alaba da Trent da Asencio da A. Carreras da Fran García, da kuma Huijsen.
Yayin da yan wasan tsakiyar fili suka hada da Valverde da Tchouameni da Arda Güler da Ceballos da kuma matashin dan wasa Thiago Pitarch wanda ke da shekaru 18.
Yan wasan gaban fili kuwa sun hada da Vini Jr. da Mbappe da Rodrygo da Gonzalo da Brahim da kuma Mastantuono.
Za’a dai a gabatar da wasan ne a filin wasa na Santiago Bernabeu, da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya.









