LabaraiSiyasa

Fitar Atiku daga jam’iyyar PDP ba sabon abu ba ne, muna sa ran dawowarsa nan gaba – inji Damagum

Shugaban riko na jam’iyyar PDP, Umar Damagum, ya bayyana cewa fitar tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya daga jam’iyyar ba sabon abu ba ne kuma bai zo musu da mamaki ba.

Damagum wanda ya bayyana haka a jihar Bauchi a yayin da ya ke zantawa da manema labarai, ya ce ko kaɗan jam’iyyar ta PDP ba ta damu da fitar ɗan takarar na ta ba, domin kuwa a baya ya fita daga jam’iyyar ya kuma sake dawowa cikin ta.

Umar Damagum ya bayyana matakin barin jam’iyyar da Atikun yayi a matsayin wani salo na neman biyan bukatun siyasar sa da ya sanya a gaba.

Karo na uku kenan dai da Atiku Abubakar ke bayyana ficewa daga jam’iyyar PDP, a inda a karon farko a kokarin sa na neman shugabancin ƙasa a zaɓen shekara ta 2007, ya bar jam’iyyar a shekara ta 2006 a inda ya bar PDP zuwa jam’iyyar AC, wacce daga baya ta koma ACN.

Sai kuma shekara ta 2014, a lokacin da Atiku ya sake bankwana da jam’iyyar PDP bayan ya dawo cikin ta a shekara ta 2009, a inda ya koma jam’iyyar APC.

Sai dai kuma a shekara ta 2017, Atiku Abubakar ya bar jam’iyyar ta APC a inda ya sake komawa PDP, wacce a yanzu haka ya bada sanarwar ficewa daga cikin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button