KasuwanciLabaraiTattalin Arziki

Da wuya a iya gyara matatun man fetur ɗin Najeriya – inji Dangote.

Fitattacen attajiri mamallakin shugaban gungun kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina barnatar da kuɗin al’ummar Najeriya wajen kokarin gyaran matatun man ƙasar, yana mai cewa da wuya matatun su dawo aiki kamar yadda ake bukata.

Dangote wanda ya shaida haka a yayin da ya karbi bakuncin ɗaliban Babbar cibiyar nazarin kasuwanci ta nahiyar Afrika dake jihar Legas, ya bayyana cewa duk da makudan kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta samar domin gyaran matatun man, amma har izuwa wannan lokaci matatun man basa aiki.

Hamshakin ɗan kasuwar ya kuma tuna yadda a baya gwamnatin tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo tayi kokarin siyar masa da matatun domin amfanin yan Najeriya, amma kamfanin mai na ƙasa a lokaci shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya nuna adawa akan yin hakan, lamarin da ya sa ala -tilas ya janye daga yarjejeniyar da aka kulla tare da mayar wa da gwamnatin tarayya matatun man ta.

A baya bayan dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta kashe sama da dalar Amurka biliyan goma sha takwas wajen gyaran matattun man, sai dai kuma hay zuwa wannan lokaci matattun basa iya samar da man fetur domin amfanin al’ummar Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button