
A cigaba da wasannin sharar fagen neman kaiwa ga gasar firimiya lig ta kasa da ake gabatarwa tsakanin ƙungiyoyin takwas na gasar NNL, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau Academy tayi canjaras da Wikki Tourists a zagaye wasa na biyu da ƙungiyoyin suka fafata a filin wasa na Stephen Keshi sake birnin Asaba na jihar Delta.
Rahotanni sun yi nuni da cewa dukkanin ƙungiyoyin biyu sun nuna bajinta sai dai kuma haka aka kamalla wa’adin lokacin wasa na minti casa’in ba tare da an samu ƙungiyar da ta samu nasara zura ƙwallon a raga ba.
A wasan farko na shiryar arewa da aka gabatar da safiyar wannan rana, Yobe Desert Stars ce ta lallasa Doma United daci biyu da daya.
Zuwa yanzu dai Yobe Desert Stars ita ce akan gaba a shiyyar arewa da yawan maki huɗu daga wasanni biyu yayin da Barau Academy da kuma Wikki Tourists suka kasance a mataki na biyu da yawan maki biyu sai kuma Doma United a mataki na huɗu da maki guda.
Wannan dai na nuni da cewa har yanzu dukkanin ƙungiyoyin huɗu na da daman kaiwa ka shiga gasar ta Firimiya Lig idan suka yi nasara a wasan ƙarshe da za’a gabatar a ranar Alhamis 10 ga wannan watan.
Ƙungiyoyi biyu ne daga kowacce shiyya zasu haura zuwa gasar Firimiya Lig ta kasa.









