LabaraiSiyasa

Gwamnan jihar Filato yayi wa kwamitin zartarwar gwamnatin sa garambawul.

Gwamnan Nijar Filato, Caleb Mutfwang ya sauke Kwamishinonin sa biyar daga ƙunshin kwamitin zartarwar jihar.

A wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Filato, Architect Samuel Jatau, ya bayyana sunayen Kwamishinonin da aka sauke da suka hada da Chrysanthus Dawam da Noel Nkup da Jamila Tukur da Obed Goselle da kuma Sule Musa.

Duk da cewa ba’a bayyana dalilan da ya sanya gwamnan ɗaukar wannan matakin ba, manazarta na ganin hakan baya rasa nasaba da gazawar Kwamishinonin wajen gudanar da ayyukan su.

Ko a baya dai sai dai gwamnan ya dakatar da biyu daga cikin Kwamishinonin da ya sallama, Chrysanthus Dawam da Jamila Tukur na tsawon watanni uku bisa wasu dalilai da ba’a bayyana ba.

A wani labarin kuma, gwamnan na jihar Filato, Mutfwang, ya aminci na naɗin sabbin Kwamishinoni biyar da suka hada da Sunday Alex daga karamar hukumar Bassa, Joyce Ramnap daka Langtang ta kudu da Sylvanus Dongtoe daga karamar hukumar Shendam da Nicholas Baamlong da kuma Cornelius Doeyok, dukkanin su daga Qua’an Pam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button