LabaraiWasanni

WAFCON: Hukumar CAF ta kara adadin kyautar kuɗin da za’a bawa Kasar da ta lashe gasar a bana.

Hukumar Wasan Kwallon ƙafa ta nahiyar Afrika, CAF ta bayyana kyautar dalar Amurka Miliyan guda ga duk ƙasar da ta lashe gasar mata da ake gabatarwa a tsakanin ƙasashen Afrika a yanzu haka a ƙasar Moroko.

A wata sanarwa da shugaban hukumar CAF, Dr Patrice Motsepe ya sanyawa hannu ta bayyana cewa, a wani mataki da hukumar ta dauka domin inganta harkokin wasan ƙwallon ƙafa a tsakanin mata, hukumar ta yi kari akan yawan ƙyautar kudin da ake bawa ƙasashen da suka taka rawa a gasar daga wannan shekarar.

A cewar Patrice Motsepe, daga yanzu duk ƙasar da tayi nasara za ta karbi ƙyautar tsabar kuɗi Dalar Amurka Miliyan guda, yayin da ƙasar da ta kasance ta biyu za ta amshi dalar Amurka dubu dari biyar a matsayin kyauta. Sai kuma ƙasar da ta zo ta uku, da za ta rabauta da Dalar Amurka dubu dari uku da hamsin, yayin da ƙasar da ta zo ta hudu za ta karbi dala dubu dari uku.

Sauran kyaututtukan da hukumar ta CAF ta bayyana bayarwa sun hada da ƙyautar Dalar Amurka dubu dari biyu ga ƙungiyoyi huɗu da suka bar gasar a matakin wasan dab dana kusa dana ƙarshe watau Quarter finals, yayin da ƙasashen da suka kasance a matsayi na uku a rukuni zasu karbi Dalar Amurka dubu dari da hamsin, sai kuma ƙasashen da suka kasance a matsayi na hudu wanda zasu koma gida da kyautar dalar Amurka dubu dari da hamsin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button