
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Mata ta Najeriya za ta fafata da takwararta ta Ƙasar Moroko a wasan ƙarshe na cin kofin tamaula na ƙasashen nahiyar Afrika wanda za’a gabatar a ranar Asabar 26 ga wannan watan.
Najeriya ta kai ga wasan ƙarshe ne biyo bayan nasarar da ta samu akan ƙasar Afrika ta Kudu da ci biyu da daya da yammacin jiya Talata.
Wannan dai shine karo na gona sha shida da Super Falcons na Najeriya ke samu nasara akan Bayana-Bayana na Afrika ta Kudu.
A daya bangaren kuma, Moroko ta samu nasara akan ƙasar Ghana da ci hudu da uku ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron raga watau ‘Penalty’ biyo bayan kammala wa’adin mintuna casa’in na wasa da kuma karin mintuna 30 na karin lokaci, watau extra time, kowacce ƙasa na da ci guda.
Ƙasashen biyu dai sun fafata da juna a irin wannan gasar a shekara ta 2022, a inda Moroko tayi nasara akan Najeriya wasan kusa dana ƙarshe.
Gabanin wasan ƙarshe da za’a gabatar a ranar Asabar, akwai wasan neman gurbin na uku da za’a fafata a ranar Juma’a tsakanin Afrika ta Kudu da kuma ƙasar Ghana.









