KimiyyaLabarai

Dutse mai aman wuta ya janyo tserewar mazauna wani kauye a Habasha

Ɗaruruwan mutane ne a ga wani ƙauye na Habasha mai tazarar kilomita 165 daga arewa maso gabashin babban birnin kasar Addis Ababa, ke barin gidajensu sakamakon wani dutse mai aman wuta.

Wani bidiyo da cibiyar nazarin ƙasa ta Habasha ta wallafa a shafinta na Facebook, ya nuna yadda tururi ke fitowa daga dutsen.

A cikin ƴan makonnin nan, an samu afkuwar girgizar ƙasa fiye da goma a kusa da Awash Fentale – wani yanki da ke fama da girgizar ƙasa a lardin Afar na Ethiopia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button