LabaraiSiyasa

Gwamnan jihar Osun ya ƙaryata jita-jitar cewa zai koma jam’iyyar APC

A karon farko, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana matsayin sa na kasancewa cikakken ɗan jam’iyyar PDP, yana mai cewa rade-radin da ake yi na cewa zai bar jam’iyyar zuwa APC bashi da tushe.

Gwamnan wanda ya bayyana haka a yayin da yake kaddamar da aikin titin cikin garin Ila, ya kuma tabbatar da cewa yana nan a jam’iyyar da al’ummar jihar Osun suka zaɓe shi a cikin ta a matsayin gwamnan jihar.

“Nayi alƙawarin cewar zanyi aiki tukuru a matsayin gwamnan jihar Osun a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar mu ta PDP, a don haka babu wani dalili da zai sa na kaucewa wannan manufa” a cewar Adeleke.

Daga nan gwamnan ya bayyana irin ayyukan da gwamnatin sa ta aiwatar tare da bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta cigaba da iyakar kokarinta na ganin ta cika dukkanin alƙawuran da ta ɗauka a yayin yaƙin neman zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button