Tallafin man fetur hanya ce ta sace kuɗin al’umma – tsohon shugaban EFCC, Bawa.

Tsohon Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana yadda aka yi amfani da batun tallafi man fetur wajen sace biliyoyin kuɗin al’ummar Najeriya.
Abdulrasheed Bawa, a wani littafi da ya rubuta wanda ya mayar da hankali wajen bankaɗo tare da bayyana hanyoyin da ake amfani dasu wajen aikata almundahana da sunan samar tallafin man fetur, ya lissafa hanyoyi da dama da yan kasuwa da haɗin bakin ma’aikatan gwamnati ke amfani da su wajen yin sama da fadi da dukiyar ƙasa da sunan tallafi.
Bawa wanda ya jagoranci shugabancin hukumar a lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari a tsakanin shekara ta 2021 zuwa 2023, ya bayyana yadda a wasu lokutan yan kasuwa ke amfani da takardun izinin ciniki na man fetur wajen karba tallafi fiye da sau daya, yayin da a hannun guda ake kai man da aka bada tallafi akan sa zuwa kasuwannin bayan-fage domin cin kazamar riba.
Littafin mai suna “The Shadow of Loot & Losses: Uncovering Nigeria’s Petroleum Subsidy Fraud,” a turance, ya kuma bayyana yadda kamfanonin da ke hada haɗar man fetur ke yin karin akan adadin yawan man fetur ɗin da suka shigo dashi ƙasar nan domin karbar tallafi, yayin da hannun guda wasu ke karɓar kuɗin tallafi da takardun karya ko na bogi.









